13 Faburairu 2022 - 13:39
Sudan : Sojoji Sun Ce Sun Shirya Tattaunawa Domin Mika Mulki

Shugaban gwamnatin rikon kwaryar soji a Sudan, Abdel Fattah Al-Burhan, ya jaddada cewa, kofar sojojin kasar a bude take domin shirya tattaunawa ta kasa da nufin cimma nasarar mika mulki ga gwamnatin demokaradiyya a kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA -A yayin wata tattaunawar shugaban da aka watsa ta gidan talabijin na Sudan TV, Al-Burhan ya ce, sojojin kasar a shirye suke su gudanar da tattaunawa game da wa’adin mika mulki a kasar muddin aka cimma matsaya.

Ya ce, “Ko ni ko kuma hukumar sojojin kasar, babu wanda yake son dawwama a mulkin Sudan.

Sojojin zasu sakarwa fagen siyasar kasar mara da zarar an yi nasarar gudanar da zabuka ko kuma an cimma maslaha a kasar."

Ya yi kiran a shiga tattaunawa wadda zata kunshi dukkan bangarorin kasar, amma ban da jam’iyyar National Congress Party, ta tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir.

342/